ABNA24 : Yayin wani taron manema labarai na hadin gwiwa, biyo bayan tattaunawarsa da shugaban Mali Bah N’Daw dake ziyara a kasar, Shugaba Tebboune ya ce a shirye suke su taimakawa ‘yan uwansu na Mali, dangane da abun da suke ganin ya dace da tabbatar da zaman lafiya gabanin zaben kasar dake tafe, kamar yadda suka tsara.
A nasa bangaren, shugaban Mali, ya bayyana gamsuwarsa da sakamakon ziyarar aiki da ya yi a Aljeriya, yana mai cewa, rikicin kasarsa na da sarkakiyar da ba za a iya shawo kansa ba tare da neman taimakon abokai ba.
Tun a shekarar 1991, Aljeriya ke bada gudunmuwa cikin kokarin kasashen duniya dake da nufin tabbatar da zaman lafiya da shawo kan matsalar kudi a Mali.
Haka kuma, ita ke jagorantar kwamitin dake bibiyar yarjejeniyar sulhu da wanzar da zaman lafiya a Mali.
342/